Connect with us

News

NJC Ta Dakatar Da Alkalai Uku, Ta Bude Bincike Kan Wasu 27

Published

on

njc building

Hukumar Kula da Harkokin Shari’a ta Kasa (NJC) ta dakatar da wasu alkalai uku daga bakin aiki na tsawon shekara daya ba tare da biyansu albashi ba, saboda zargin aikata rashin da’a.

Wadanda abin ya shafa su ne:Mai Shari’a Jane E. Inyang na Kotun Daukaka Kara a Uyo,Mai Shari’a Inyang Ekwo na Babbar Kotun Tarayya a Abuja,da Mai Shari’a Aminu Baffa Aliyu na Babbar Kotun Tarayya a jihar Zamfara.

Advertisement

JAMB Ta Ce Ba Ta Da Alaka da Shafin Da Ke Karɓar Kuɗi Daga Hannun Ɗaliban Da Suka Rasa UTME

Sanarwar da NJC ta fitar bayan taronta na 108 da ta gudanar a ranar 30 ga Afrilu, ta ce an dauki matakin ne bisa binciken da aka gudanar kan aikinsu.

A cewar NJC, Mai Shari’a Jane E. Inyang an same ta da laifin bayar da umarnin sayar da wani kamfani a lokacin da shari’a na kan gudana – lamarin da ya sabawa dokokin da’a.

Advertisement

Shi kuwa Mai Shari’a Ekwo, an ce ya aikata wasu abubuwa da suka saba wa dokar aiki. Bayan dakatarwar shekara daya, an kuma sanya shi cikin jerin wadanda za a sa ido a kansu na tsawon shekaru biyar tare da hana shi karin girma a wannan lokacin.

Mai Shari’a Baffa Aliyu na Zamfara an samu shi da laifin hana jami’an tsaro gudanar da aikinsu a wata shari’a da ke gaban kotunsa. Shi ma an dakatar da shi na shekara daya tare da sanya shi cikin jerin alkalai da za a rika lura da su har na tsawon shekaru uku.

Advertisement

Baya ga hakan, NJC ta umurci Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, da ya soke nadin da ya yi na Mukaddashin Babban Alkalin Jihar, Mai Shari’a Theophilus Nnamdi Nzeukwu. Haka kuma ta bukaci wasu manyan alkalai a jihar su bayyana hujjojin su ko su fuskanci ladabtarwa.

Hukumar ta ce ta kafa kwamitoci tara da za su binciki alkalai 27 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban.

Advertisement

NJC ta kuma yi watsi da wasu korafe-korafe 29 da aka shigar gabanta saboda rashin tushe, yayin da ta fitar da wasikar gargadi ga wani mai shari’a a Legas.

A bangare guda kuma, NJC ta fara nazarin wata kara da wani Mahmud Aliyu ya shigar kan nadin alkalai a Zamfara, inda ya zargi hukumar jihar da son zuciya da karya ka’idojin tantancewa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending