Connect with us

News

Kotu Ta Tura Amarya Da Angonta Gidan Yari A Kano 

Published

on

images (2)

Wata babbar kotun Shari’ar Musulunci da ke Kano ta tura wata mata da sabon mijinta gidan yari na tsawon mako guda, bayan ta amsa cewa ta yi aure a kan aure.

Kotun da ke zamanta a Post Office, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Munzali Tanko Soron Dinki, ta yanke wannan hukunci ne bayan jin karar da wani magidanci ya shigar, yana zargin matarsa da yin aure da wani mutum duk da cewa bai sake ta ba.

Advertisement

Atiku: Ba Kai Za Ka Yanke Wa Matasa Shawara Ba — Adnan Ya Fadawa Baba-Ahmed”

DALA FM  ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a unguwar Tudun Murtala da ke Kano, lokacin da mijin ya kai ziyara gidan matarsa, inda ya iske wani mutum kwance a gadonta.

A cewar sa, sai da ya tambaye su matsayin su, inda matar ta ce mutumin da ke gadon dan uwanta ne. Amma daga bisani sai mijin ya gayyato makota suka zo suka shaida abin da ke faruwa, kafin ya garzaya kotu domin shigar da kara.

Advertisement

A gaban kotu, mijin ya bayyana cewa har yanzu yana da aure da matar, kuma har kwana biyu da suka gabata suna tare da ita. Sabon mijin kuwa ya ce matar ta fada masa cewa ba ta da aure, kuma ya biya sadakinta na Naira dubu 100 kafin a daura auren.

Lokacin da kotu ta tambayi matar ko za ta rantse cewa tsohon mijin nata ya sake ta, sai ta ce ba za ta iya rantsewa ba. Haka kuma ta hana tsohon mijin daga rantsewa cewa har yanzu suna da aure.

Advertisement

Daga nan ne kotu ta bukaci jami’an tsaro su tafi da su. A lokacin, matar ta ce za ta fadi gaskiya. Sai ta bayyana wa kotu cewa hakika ta yi aure a kan aure, sannan ta nemi gafara.

Mai Shari’a Munzali Tanko Soron Dinki ya ce wannan laifi ne mai tsanani a shari’ar Musulunci, sannan ya bayar da umarnin a tura su gidan gyaran hali na tsawon mako guda domin horo da nazari.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending