Connect with us

News

An Kashe Sama Da Mutane 1,700 A Rikicin Iyakoki Da Muhalli A Najeriya — RAHOTO 

Published

on

communal clash

Akalla mutane 1,796 ne suka rasa rayukansu sakamakon rikicin iyaka da na al’umma a sassa daban-daban na Najeriya daga Janairu 2018 zuwa Agusta 2025.

Wannan na cikin bayanan da wata ƙungiya mai zaman kanta, Foundation for Partnership Initiatives in the Niger Delta (PIND), ta fitar, wadda ke bibiyar rikice-rikice musamman a yankin Neja Delta.

Advertisement

SERAP Da Wasu Ƙungiyoyi 55 Sun Nemi Akpabio Ya Sauka Daga Kujerar Shugaban Majalisar Dattawa

Rahoton ya nuna cewa daga shekarar 2018 zuwa 2022, mutum 676 ne suka mutu a irin wadannan rikice-rikice, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Amma daga 2023 zuwa 2025, yawan mace-macen ya karu matuƙa, musamman a yankunan Kudu da Arewa ta Tsakiya.

Advertisement

A jihar Cross River kaɗai, an samu sama da mace-mace 400 tsakanin Janairu 2020 da Disamba 2023 sakamakon rikicin ƙasa.

Haka zalika, fiye da mutum 650 ne suka mutu a jihohin Delta da Bayelsa sakamakon rikicin iyaka da ƙasa.

Advertisement

PIND ta ce rikicin Okuama da ya auku a jihar Delta da kuma na Igbomotoru a Bayelsa, wanda ya haɗa da jami’an tsaro, na iya ci gaba idan ba a ɗauki mataki ba.

Haka nan kuma rahoton ya lissafa wasu manyan hare-hare da suka hada da kisan mutane 14 a Agbudu da ke Kogi, da kuma rikicin fili a jihohin Benue da Enugu.

Advertisement

Masana tsaro sun ce gazawar aiwatar da Dokar Amfani da Ƙasa (Land Use Act) da kuma rashin fayyace iyakokin ƙasa ne ke haddasa yawaitar wadannan rikice-rikicen.

 

Advertisement

PUNCH

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending