News
SERAP Da Wasu Ƙungiyoyi 55 Sun Nemi Akpabio Ya Sauka Daga Kujerar Shugaban Majalisar Dattawa
Ƙungiyoyi 56 na fararen hula, ciki har da Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP), sun bukaci Sanata Godswill Akpabio da ya yi murabus daga kujerar Shugaban Majalisar Dattawa, bayan hukuncin kotu da ya tabbatar da maguɗin zaɓen da ya haifar da nasararsa a 2019.
Sanarwar ta ƙungiyoyin, wadda ta haɗa da CISLAC da CJID, ta ce hukuncin Kotun Daukaka Ƙara da ke Calabar ya tabbatar da hukuncin ɗaurin shekaru uku da aka yanke wa Farfesa Peter Ogban bisa samunsa da laifin sauya sakamakon zaɓe don amfanin Akpabio, wanda ya tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar APC.
Kungiyoyin sun ce, “Hukuncin kotun ya kassara sahihancin kujerar da Akpabio ke rike da ita. Don haka ya dace da mutunta adalci da dimokuradiyya, ya sauka daga mukaminsa.”
Duk da cewa babu wata hujja kai tsaye da ke nuna cewa Akpabio ya da hannu wajen maguɗin, ƙungiyoyin sun ce samunsa da nasara ta hanyar zaɓe marar inganci ya lalata amincewar da ya samu daga al’umma.
Sun kuma jinjinawa INEC da tsohon kwamishinan zaɓe na jihar Akwa Ibom, Mike Igini, bisa tsayawarsu tsayin daka wajen kare gaskiya da adalci. Haka kuma, sun bukaci a sake fasalin tsarin zaɓen ƙasar gaba ɗaya domin magance irin wannan matsala a nan gaba.
-
News3 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
