News
Matashi Ya Kashe Saurayin ’Yar Uwarsa A Kano
Wani matashi mai shekaru 25, Mansur Umar, ya shiga hannun ’yan sanda bisa zargin kashe Sulaiman Musa, saurayin ’yar uwarsa, a unguwar Kunya da ke karamar hukumar Minjibir ta Jihar Kano.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar.
Ingila Ta Rage Tsawon Lokacin Bizar Aikin Bayan Kammala Karatu Watanni 18.
Ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:30 na dare, a ranar Juma’a, 9 ga watan Mayu, 2025, lokacin da Sulaiman Musa, wanda shima ke da shekaru 25, ya kai ziyara wajen budurwarsa, Fiddausi Umar, a gidansu.
“An zargi Mansur Umar da kai masa dukan sanda a kai, wanda ya jikkata shi matuka. An garzaya da shi Asibitin Kunya, daga nan kuma aka mika shi Asibitin Koyarwa na Murtala Muhammad da ke Kano, inda aka tabbatar da rasuwarsa da misalin karfe 12:50 na safiyar Asabar,” in ji Kiyawa.
Ya kara da cewa an tsare wanda ake zargi yayin da Sashin Binciken Kisan Kai na rundunar ke ci gaba da gudanar da bincike.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana damuwarsa kan faruwar lamarin, tare da yin kira ga matasa da su rika amfani da hanyoyin fahimtar juna da sulhu maimakon daukar doka a hannu.
Ya kuma bukaci jama’a da su ci gaba da ba da hadin kai wajen kawo rahotannin duk wani abu da ke da alamar barazana ga zaman lafiya a jihar.
