News
Kotu zata fadi yiwuwar bada belin Malam Abduljabbar a zama na gaba.

Daga maryam bashir musa
A cigaba da shari’ar Malamin Addinin Musulunci Sheikh Abduljabbar Kabara, Alƙali Ibrahim Sarki Yola ya bayyana cewa zai fadi ra’ayin sa akan bada belin Malamin a zama na gaba.
Ya fadi hakan ne yayin da Lawyan Malamin ya bukaci kotu ta bada belin sa duba da matsayin da aka kawo cikin shari’ar a yanzu.
”Kafin a tashi ina da roko, rokon namu shine a dagawa ta baya kusan biyu ko uku da suka gabata, kotun nan tace insha Allahu zata duba yiwuwar bada belin wanda ake kara, a matsayin da muka isa yanzu, muna rokon kotu ta bada belin sa. Duk sharadin da kotu zata saka, wanda ake ƙara zai iya cika su da yardar Allah. Shifa hurumin bada beli iko ne na kotu, wannna shine rokon mu.” Inji Barista Auwal Muhammad, lawyan dake kare Malam Abduljabbar.
A nasu bangaren, lawyoyin gwamnati ta bakin Barista Sa’ida Shu’aibu SAN yayi suka akan wannan roko na bada belin Malamin.
”Muna nan akan bakar mu ta suka. Dalili na farko shine cewar Tuhumar, tuhuma ce da ta danganci za a iya zartar da hukuncin kisa, saboda haka a ka’idar doka ta ACJL 2019, ba a bada beli. Na 2 kuma, kuma shine ma na karshe. Har an shiga gaɓar kariya, babu wani dalili da ya nuna za a iya bada beli, ita dokar ACJL sashe na 171 (1) cewa tayi wanda ake tuhuma da in an tabbatar da laifi hukuncin kisa ne, baza a bashi beli ba. Dan haka bamu yarda a basu wannan belin ba. ina rokon kotu tayi watsi da rokon.” inji Barista Sa’ida Shu’aibu SAN
Lawyan wanda ake ƙara ya sake maida martani da jaddada rokon su akan neman belin wanda ake ƙara.
”Ai dokar cewa tayi in an tabbatar, to ba wanda zai tabbatar in ba wannan kotu ba. Kundin Tsarin Mulkin Kasa Sashe na 36 karamin sashe na 6 ya bayyana cewa duk wanda aka kawo kotu, bai da laifi, kotu ce kadai zata tabbatar. Saboda haka sukar da sukai, muna rokon kotu tayi watsi da shi, ta amshi wanna roko namu ta bada wanda ake ƙara a hannun beli. ” inji Barista Auwal Muhammad
Yayin da kotu tayi haka, Mai Shari’a Alƙali Ibrahim Sarki Yola ya ce zai fadi matsayin sa akan wannan roko na beli.
”Dangane da wannan roko, na barshi ba zance komai ba a yanzu saboda lokaci ya ja, sai a rana ta gaba, ranar 31/3/22 In Allah ya yarda. ” Inji Mai Shari’a.
Ya dage zaman zuwa ranar Alhamis 31/3/22.
