Connect with us

News

Yadda Tinubu Da Barau Suka Taimaka Wajen Kafa Rundunar Tsaron Daji A Najeriya

Published

on

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu a kan dokar kafa Nigeria Hunters Forest Security Service (NHFSS), domin fatattakar ’yan ta’adda da masu laifi daga dazukan Najeriya.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya taka rawar gani wajen ganin an amince da dokar cikin hanzari. Wannan ya biyo bayan ganawar da ya yi da shugabannin NHFSS inda ya nuna muhimmancin rundunar wajen kare kasar daga barazanar tsaro.

Advertisement

‎Kungiyar ‘Yan Asalin Kano da ke Arewa Maso Gabas Ta Yaba da Jagorancin Sanata Barau

A lokacin da Babban Kwamandan NHFSS, Dr Joshua Osatimehin, ya kai masa ziyara, Sanata Barau ya ce, “Najeriya na bukatar rundunar da za ta fatattaki masu aikata laifuka a daji.”

Bayan nan ne Barau ya yi alkawarin matsa wa shugaban kasa lamba domin ya amince da dokar, abin da ya cika cikin kasa da wata biyu.

Advertisement

Shugaban kasa ya umarci a dauki sabbin jami’ai da za a horar tare da basu kayan aiki, domin tabbatar da nasarar aikin. Ma’aikatar Tsaro da ta Muhalli za su sa ido a kan aikin rundunar tare da hadin gwiwar jihohi.

Tun kafin amincewar dokar, NHFSS ta shirya horo a Abuja tare da hadin gwiwar jami’an DSS, Sojoji, ’Yan Sanda da NDLEA. Kwamishinan ’Yan Sanda na Abuja, CP Ajao Adewale, ya ce hadin gwiwar hukumomin tsaro ne mafita ga matsalolin da ke cikin dazuka.

Advertisement

Sanata Barau ya ce dazukan Arewa za su iya zama wurin yawon bude ido da ci gaban muhalli idan aka kare su daga barazanar masu laifi. Ya kuma yabawa Shugaba Tinubu da Majalisar Tarayya bisa goyon bayan dokar.

A yanzu, doka ta kafa rundunar NHFSS ta fara aiki da nufin kawo sauki a fannin tsaro, musamman a yankunan da suka fi fuskantar barazana.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending