Connect with us

News

IPAC Ta Ce Dakatar Da Shirye-shiryen Siyasa Kai Tsaye  Hanya Ce Ta Wanzar Da Daidaito A Kano

Published

on

Jami’an Tsaro Sun Fi Kowa Hantarar Yan Jarida

Kungiyar Tuntuba ta Jam’iyyu (IPAC) reshen jihar Kano ta bayyana gamsuwa da matakin da wasu gidajen rediyo da talabijin a jihar suka ɗauka na dakatar da shirye-shiryen siyasa da ake watsa su kai tsaye.

Shugaban IPAC na jihar Kano, Alhaji Isah Nuhu Isah, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a birnin Kano a ranar Lahadi. Ya ce matakin da kafafen yada labaran suka ɗauka ya zo a kan gaba wajen tabbatar da zaman lafiya da kare martabar aikin jarida.

Advertisement

Peter Obi Na Iya Zama Abokin Takarar Atiku A 2027

“Wannan mataki da kafafen yaɗa labarai suka ɗauka ya nuna irin kishin ƙasa da kuma hangen nesa da ke cikin al’umma. A zamanin da ake fama da kalaman rarrabuwar kai da yada labaran ƙarya, wannan yunkuri abin a yaba ne,” in ji shi.

Isah ya bayyana cewa, dakatar da shirye-shiryen siyasa kai tsaye zai taimaka matuƙa wajen rage yaduwar kalaman da ka iya tayar da zaune tsaye da haddasa rikici, musamman a wannan lokaci da al’umma ke cikin damuwa da gajiya da siyasa.

Advertisement

Ya ce IPAC a matsayinta na kungiya mai lura da dangantakar jam’iyyu, na goyon bayan duk wani mataki da zai tabbatar da cewa siyasa na gudana cikin mutunci da girmama juna. “Mun dade muna kira da a dakile maganganun da ke kawo rikici da tada hankali a cikin shirye-shiryen siyasa, musamman wadanda ake watsa su kai tsaye ba tare da tacewa ba,” in ji shi.

Shugaban IPAC ya yi nuni da cewa a lokuta da dama shirye-shiryen siyasa sun koma matsugunin batanci da zagin juna, maimakon su kasance dandalin tattaunawa da fito da ingantattun manufofi ga al’umma.

Advertisement

“Ana buƙatar kafafen yaɗa labarai su riƙa ɗaukar nauyin da ya rataya a wuyansu wajen tabbatar da gaskiya da ɗorewar zaman lafiya, ba wai su zama kayan aiki wajen rura wutar rikici ba,” in ji shi.

Ya kuma bayyana cewa IPAC tana shirin haɗa gwiwa da kafafen yaɗa labarai, kungiyoyin fararen hula, hukumomin tsaro da jam’iyyun siyasa domin samar da tsarin da zai tabbatar da cewa duk wani shirin siyasa da ake watsa wa ya zama na ƙwarewa da dacewa da bukatun jama’a.

Advertisement

“Za mu tuntuɓi dukkan masu ruwa da tsaki domin tsara hanyoyin da za su tabbatar da cewa an koma tsarin siyasa na kishin ƙasa da girmama juna,” in ji shi.

 

Advertisement

A ƙarshe, IPAC ta yaba da gwiwa da kwarin guiwar da kafafen yaɗa labarai suka nuna, inda ta bayyana matakin a matsayin wani nau’i na hidima ga ƙasa da ƙarfafa ginshikan dimokuraɗiyya a jihar Kano.

Matsayar IPAC na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da bayyana damuwa kan yadda kalaman batanci ke ƙara yawaita a fagen siyasar Najeriya, tare da rawar da kafafen yaɗa labarai ke takawa ko dai wajen ƙara rura wutar rikici, ko kuma daidaita lamarin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending