Uncategorized
Peter Obi Na Iya Zama Abokin Takarar Atiku A 2027
Rahotanni sun bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a PDP, Atiku Abubakar, na cigaba da tattaunawa da Peter Obi kan yiwuwar yin takara tare a zaɓen 2027.
Wata majiya ta shaida wa PUNCH cewa Atiku ya miƙa tayin kujerar mataimakin shugaban ƙasa ga Obi, a wani yunƙuri na kafa ƙawance domin kalubalantar shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓe mai zuwa.
Hawan Jini: Gwamnatin Kano Ta Kara Kaimi Wajen Yaki Da Cututtuka Masu Zaman Kansu
Majiyar ta ce an fara wannan tattaunawa ne tun farkon shekarar nan a ƙasar Birtaniya, inda Atiku ya sha alwashin yin wa’adi na shekara huɗu kacal, kafin ya mika mulki ga Obi idan suka samu nasara.
A shekarar 2019, Obi ya tsaya takarar mataimakin shugaban ƙasa tare da Atiku a jam’iyyar PDP, amma suka sha kaye a hannun Shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC.
A watan Maris da ya gabata, Atiku da Obi da wasu jiga-jigan siyasa sun haɗu a Abuja suka kafa wani ƙawance domin fuskantar APC a 2027
Sai dai ƙawancen ya jawo ce-ce-ku-ce, musamman ganin rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyun PDP da LP,
Wata majiya ta ce ana duba yiwuwar amfani da jam’iyyar ADC a matsayin wani sabon dandali idan har rikice-rikicen ba su samu mafita ba.
Duk da haka, shugabannin ADC sun ce za su bayyana matsayarsu kafin ƙarshen mako.
A gefe guda, wasu masu fashin bakin siyasa na ganin cewa lokacin Atiku ya wuce, yayin da wasu ke ganin haɗin gwiwarsa da Obi na iya haifar da tasiri a zaben 2027.
