News
Jami’an Yan Sanda Sun Bankaɗo Masana’antun Takin Bogi A Bauchi
Rundunar ’Yan sanda a jihar Bauchi ta yi nasarar bankaɗo wasu masana’antun bogi da ke sarrafa takin zamani da magungunan ciyawa na jabu.
Jami’an tsaron sun kai samame a wuraren ne bayan samun bayanan sirri, inda suka kama mutane biyar da ake zargi da hannu a harkar.
An Sanya Ladan Naira Miliyan 5 Ga Wanda Ya Bankado Fursunonin Da Suka Tsere
A ranar 10 ga watan Mayu, 2025, ’yan sanda sun kama wani mutum mai suna Muhammad Abubakar, ɗan shekara 34, a kasuwar Magaji Quarters, dauke da buhunan taki na jabu.
A gidansa ne jami’an suka gano buhu shida na taki da kwalaye 46 na maganin ciyawa, da kuma wasu kayan haɗa sinadaran bogi.
Da aka fara bincike, Muhammad ya amsa laifinsa, inda ya bayyana sunan wani abokinsa mai suna Abubakar Umar, ɗan shekara 24, wanda daga bisani aka kama shi.
WIKKI TIMES ta ruwaito cewa a wani farmaki daban da suka kai, an kama wani Anas Abubakar, ɗan shekara 32, a shagon sa da ke kan hanyar Gombe, inda aka samu buhuna 44 da rabi na taki maras inganci.
Anas ya ce yana karɓar kayan ne daga wani Abdulrahman Muhammad, ɗan shekara 24, wanda ke zaune a Bakaro Quarters.
Jami’an tsaron sun bibiyi bayanin har suka isa Natsira Hamlet, kusa da ƙauyen Kangare, inda aka tarar da buhuna sama da 100 na takin jabu a wata masana’anta da ake zargin mallakar Abdulrahman ce.
Rundunar ta kuma kai samame wasu masana’antun bogi guda biyu da ke hannun Sama’ila Abdullahi (34) da Mujahid Abdullahi (32), inda aka ƙwato ƙarin kayan haɗa taki da maganin ciyawa.
Kakakin rundunar ’yan sandan Bauchi, SP Ahmed Wakil, ya ce an kammala shirin gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
Ya ce rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yaƙi da masu sayar da kayan gona na bogi da ke iya jefa lafiyar manoma da amfanin gona cikin haɗari.
Wannan lamari ya faru ne a daidai lokacin da manoma ke shirin komawa gona da shigowar damina.
Masu sharhi sun ce irin waɗannan kaya marasa inganci suna jefa amfanin gona cikin matsala, sannan suna iya haddasa illa ga lafiyar jama’a da kuma barazana ga wadatar abinci a ƙasar nan.
