Connect with us

News

El-Rufai Ya Umarci Masu Neman Takarar Gwamna A Kaduna Su Ajiye Aikinsu

Published

on

Advertisements
ads

Daga Maryam bashir musa

 

 

 

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya umurci dukkan masu rike da muƙaman siyasa da ke neman takarar gwamna a 2023, su ajiye aikinsu kafin ranar 31 ga watan Maris ta 2022.

Kwamishinan kasafi da tsare-tsare, Muhammad Sani Abdullahi (Dattijo), yana daga cikin wadanda suke sha’awar gadar kujerar El-Rufai, wanda a zuwa yanzu shi kadai ne mai rike da mukamin siyasa da ya ayyana takara a cikin jami’an gwamnatin Jihar Kaduna.

Advertisement

Jaridar Daily ta ruwaito cewa akwai sauran masu rike da mukaman siyasa da suke sha’awar tsayawa takara wanda har yanzu ba su bayyana aniyarsu ba.

A cikin sanarwar da sakataren gwamnatin Jihar Kaduna, Balarabe Abbas Lawal ya fitar, ya bayyana cewa sabuwar dokar zabe da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta fitar bisa jaddawalin zaben 2023, ta nuna cewa dole duk wani mai rike da mukaman siyasa da ma’aikacin gwamnati da ke neman takarar wani ofis ya ajiye mukaminsa kafin gudanar da zaben fidda gwani.

“Bisa wannan doka muke umurtar duk wani mai rike da mukamin siyasa ya ajiye aikinsa kafin nan da kwanaki 30 lokacin da jam’iyyu za su gudanar da zabukan fidda gwani.

“Sakamakon bin wannan doka, dukkan masu rike da mukaman siyasa da ma’aikatan gwamnatin Jihar Kaduna da ke neman takara su mika wasiyar ajiye ayyukansu ga sakataren gwamnatin Jihar Kaduna kafin ranar 31 ga watan Maris ta 2022,” in ji shi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending