News
Ƴar Shekara 75 Daga Najeriya Ta Rasu A Wajen Aikin Hajji
Wata mata mai shekaru 75 da haihuwa daga Jattu Uzairue, a Karamar Hukumar Etsako ta Yamma, Jihar Edo, ta rasu yayin gudanar da aikin Hajji a Makkah.
Matar mai suna Adizatu Dazumi ta rasu ne a ranar Litinin a Asibitin King Fahad, bayan ta yi fama da gajeriyar rashin lafiya.
Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Kashe Matar Aure ‘Yar Shekara 22 A Kano
Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Edo, Alhaji Musah Uduimoh, ne ya tabbatar da rasuwar ga manema labarai a ranar Talata.
Ya ce marigayiyar ta fara rashin lafiya ne bayan ta kammala Dawafi a Ka’aba ranar Lahadi, inda aka garzaya da ita asibiti domin kula da lafiyarta.
Sai dai duk da kokarin da likitoci suka yi, Allah Ya karɓi rayuwarta da safiyar Litinin.
An yi jana’izarta kuma aka birne ta a Makkah a ranar da ta rasu, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Uduimoh ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan marigayiyar, tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar na ci gaba da kula da lafiyar sauran alhazan da ke cikin kasa mai tsarki.
