Connect with us

News

Yajin aikin ASUU: BUK ta umarci ɗalibai da su bar makarantar

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan

 

Advertisement

 

Mahukunta a Jami’ar Bayero ta Kano, BUK, sun umarci dukkanin ɗaliban da ke zaune a cikin makarantar da su bar dakunan a ranar ko kafin 20 ga watan Maris sabo da kiyaye lafiyar su.

Advertisement

Wannan umarnin na kunshe a mujallar jami’ar da a ka wallafa a Kano a ƙarƙashin jagorancin Sakataren Wallafa, Bala Abdullahi.

Abdullahi ya ce jami’ar ya ɗauki matakin ne sakamakon tsawaita yajin aikin da Ƙungiyar Malaman Jami’a ta Kasa, ASUU ta yi, inda ta ƙara wata biyu.

Advertisement

Ya ce matakin ya zo ne bayan wata ganawa da mahukunta s jami’ar su ka yi a ranar 14 ga watan Maris, inda a ka umarci duk wasu ɗalibai da ke zaune a ɗakunan cikin makarantar du fice da ga ciki.

“A na kuma sanar da ɗalibai cewa bayan ranar da s ka ce su bar ɗakunan, jami’ar za ta janye duk wasu ayyukan cikin jami’ar.

Advertisement

“An ɗauki wannan mataki ne domin kare duk wats matsala ko aikin ɓata-gari,” in ji shi.

Abdullahi ya kuma sanar da dakatar da aikin da jami’ar ta ɗauki ɗalibai su riƙa yi mata har sai an dawo karatu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending