News
Hon. Umar Faruk Mai Dattako Ya Tallafa Wa Iyalan ’Yan Siyasar Da Suka Rasu A Gwale
Ɗan siyasa a jam’iyyar APC daga karamar hukumar Gwale, Hon. Umar Faruk mai dattako, ya bada tallafin naira dubu 50 kowanne ga iyalan ’yan siyasar da suka rasu a yankin, domin rage musu radadin rashin da suka yi.
Da yake jawabi ga manema labarai a madadinsa, shugaban kwamitin raba tallafin, Aminu Sadi Bello Dorayi, ya bayyana cewa an gudanar da tallafin ne ba tare da la’akari da jam’iyyar da mamatan suka fito ba, domin a cewarsa, dukkan su ’yan siyasa ne da suka bada gudunmawa a ci gaban demokradiyya a karamar hukumar.
Rundunar ‘Yan Sanda Ta Karyata Jita-Jitar Sace Mutane 200 A Hanyar Abuja Zuwa Kaduna
“Wannan shi ne karon farko da wani ɗan siyasa ya dauki irin wannan mataki na tunawa da iyalan waɗanda suka rasu daga cikin ’yan siyasa. Mafi yawan masu rike da madafun iko na mai da hankali ne kawai kan waɗanda ke raye, amma Hon. Umar Faruk ya nuna kishin jama’a ta hanyar waiwaye da jajanta wa iyalan waɗanda suka bar mu,” in ji Dorayi.
Ya ce wannan ba zai tsaya nan ba, domin akwai shirin ci gaba da irin wannan tallafi lokaci zuwa lokaci domin tallafa wa al’umma, musamman waɗanda ke fuskantar ƙalubale a rayuwa.
Iyalan waɗanda suka ci gajiyar tallafin sun bayyana jin daɗinsu tare da yin addu’ar Allah ya saka wa Hon. Umar Faruk da alheri, tare da fatan sauran masu hannu da shuni za su yi koyi da wannan kyakkyawan misali.
