News
DA DUMI-DUMI: Gobara Ta Tashi A Wani Otel Na Alhazan Najeriya A Makkah
Wata gobara ta tashi a wani otel da ke kan titin Shara Sittin a birnin Makkah, wanda ke dauke da wasu alhazan Najeriya da suka je aikin Hajji a bana.
Sai dai, cikin ikon Allah, ba a samu asarar rai ko guda ba, domin a lokacin da gobarar ta tashi, alhazan na cikin tantunansu da ke Mina, wajen garin Makkah.
DCL HAUSA ta ruwaito cewa hukumar jin dadin alhazai ta Najeriya (NAHCON) sun tabbatar da aukuwar lamarin, tare da bayyana cewa tuni an dauki matakin gaggawa wajen samun mafita.
Wani jami’i daga NAHCON ya bayyana cewa alhazan da abin ya shafa – kimanin mutum 484 – galibinsu ‘yan International ne, wato wadanda suka biya kudin kujerarsu ta hannun kamfanonin yawon shakatawa masu zaman kansu.
Hukumomin Saudiyya sun iso wajen cikin gaggawa domin kashe wutar, kuma tuni NAHCON ta samar da wani otel na wucin gadi domin saukar da alhazan da abin ya shafa.
Za mu ci gaba da bibiyar wannan lamari, don kawo muku karin bayani.
