News
An Kama Manyan Ma’aikatan Asibiti Kan Zargin Ajalin Jarirai Saboda Sakaci
Rundunar ’Yan Sandan Chester da ke kasar Birtaniya ta cafke wasu manyan ma’aikatan asibitin Countess of Chester (CoCH) kan zargin sakaci da kuma taimakawa wata ma’aikaciyar jinya, Lucy Letby, wajen kashe jarirai a asibitin.
Rahotanni sun bayyana cewa an kama wadannan ma’aikata uku ne a ranar Talata, bayan dogon binciken da aka gudanar kan kisan jarirai bakwai da kuma yunkurin kashe wasu bakwai da aka ce Lucy Letby ta aikata tsakanin shekarar 2015 zuwa 2016.
An bai wa ma’aikatan belin wucin gadi, tare da sharadin cewa za su ci gaba da bayyana a ofishin ’yan sanda don ci gaba da bincike.
Shugaban sashen binciken manyan laifuka na rundunar ’yan sandan Chester, Paul Hughes, ya ce tuni kotu ta yanke wa Lucy, mai shekara 35, hukuncin zaman gidan yari na shekaru 15 saboda laifukan kashe jarirai da yunkurin kashe wasu.
Hughes ya bayyana cewa sakamakon binciken ya nuna akwai alamun sakaci daga bangaren wadannan manyan ma’aikatan asibitin, wanda hakan ya bai wa Lucy damar aikata laifukan ba tare da an dakatar da ita ba a wancan lokacin.
Ya ce rundunar za ta ci gaba da gudanar da bincike domin gano hakikanin rawar da ma’aikatan suka taka a wannan mummunan lamari.
A cewar jami’an binciken, an dauki lokaci mai tsawo ana tattara bayanai da hujjoji kafin a kammala kama wadannan manyan jami’an na asibitin.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
