News
Barau FC Ta Sauka Asaba Domin Fafatawa A Gasar NNL Super 8
Kungiyar kwallon kafa ta Barau FC da ke Kano ta isa birnin Asaba na jihar Delta domin shiga gasar NNL Super 8, wadda ke share fagen shiga gasar Firimiyar Najeriya (NPFL) ta kakar wasa ta 2025/2026.
Tawagar kungiyar wadda ake yi wa laƙabi da Maliya Boys ta sauka a Asaba ne a ranar Laraba, inda ta je da ‘yan wasa 32 tare da jami’ai da masu horarwa fiye da 15.
Gwamnatin Kano Ta Yabawa Gwamnatin Tarayya Bisa Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar NCC A Jihar
Jami’in yaɗa labarai na kungiyar, Ahmad Hamisu Gwale, ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.
Barau FC na fatan samun tikitin shiga gasar Firimiyar Najeriya a karon farko tun kafuwarta, inda za ta fafata da sauran ƙungiyoyi guda bakwai da suka samu nasarar zuwa wannan mataki.
Gasar Super 8 za ta gudana daga 5 zuwa 12 ga watan Yuli, 2025 a filin wasa na Stephen Keshi da ke Asaba.
An raba ƙungiyoyin gasar gida biyu – Arewa da Kudu – inda daga kudu ake da Warri Wolves, Osun United, Crown FC, Kun Khalifa FC.
Daga Arewa kuwa akwai Wikki Tourists (Bauchi), Yobe Desert Stars, Doma United (Gombe), Barau FC (Kano)
Ana sa ran daga cikin ƙungiyoyi takwas da za su buga gasar, hudu ne kawai za su samu damar hawa matakin gasar Firimiyar Najeriya (NPFL). Haka kuma za a fitar da ƙungiya guda ɗaya a matsayin zakaran gasar NNL Super 8 na shekarar 2024/2025.
A cewar Ahmad Gwale, tawagar Barau FC na da kwarin gwiwa da jajircewa wajen samun nasarar da za ta kai su ga matakin gasar manya a Najeriya.
