Connect with us

News

Lokacin Siyasa Maras Ma’ana Ya Wuce A Kano — Waiya

Published

on

waiya

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce lokaci ya wuce da za a ci gaba da siyasar banza da bata da amfani ga al’umma.

Waiya ya bayyana haka ne a ranar Juma’a yayin rantsar da sabbin shugabannin ƙungiyar masu magana a kafafen yaɗa labarai, wato GAUTA Club, a jihar Kano.

Advertisement

Ba Za Mu Bawa Kwankwaso Tikitin Takarar Shugabancin Kasa A Jam’iyyarmu Ba  —NNPP

Ya ce, “Tsarin shugabanci ba ya da alaƙa da bambancin jam’iyya. Abin da ya fi muhimmanci shi ne a samar da ci gaba da kuma tsaftace harkokin masu magana a kafafen yaɗa labarai ta yadda za su dace da zamani.”

Kwamishinan ya bayyana cewa siyasar da za ta amfani jama’a da mutunta ra’ayoyin juna ita ce siyasar da ake bukata a yanzu.

Advertisement

“Lokaci ya wuce na siyasar da ke haifar da rikici da rarrabuwar kawuna. Lokaci ne na yin siyasa da za ta ciyar da mutane gaba da amfani da dimokuraɗiyya wajen kyautata rayuwar al’umma,” in ji Waiya.

Ya shawarci masu magana a kafafen yada labarai da su rika kare mutuncin ra’ayinsu ba tare da cin zarafin wani ko ɓata masa suna ba.

Advertisement

Shugabannin GAUTA da aka rantsar su ne:

Alhaji Bashir Adamu Gaya

Advertisement

Hon. Idris Danzago

Alhaji Isa Bello Ja

Advertisement

Alhaji Ibrahim Dan Adamdam

Alhaji Damina Ali Gwarzo

Advertisement

Alhaji Auwalu Maiturare Bichi

Kwamared Rabiu Bala

Advertisement

Muhammad Idris

Hon. Danjummai Gwoska

Advertisement

Injiniya Muhammad Tarauni

Lawan Sofi Dammasanin Gaya

Advertisement

Hajiya Binta Sayyadi

Hajiya Habiba Dandalla

Advertisement

Hon. Aminu Bichi

Waiya ya ce gwamnati za ta ci gaba da goyon bayan duk wani yunkuri da zai

Advertisement

inganta aikin kafafen yada labarai a jihar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending