Connect with us

News

Ambaliyar Ruwa  Ta Fara Ɓarna A Kano Bayan Mamakon Ruwan Sama

Published

on

FB IMG 1751931289184

Ambaliyar ruwa ta fara yin ɓarna a wasu sassan jihar Kano, musamman a yankunan cikin birni, biyo bayan mamakon ruwan sama da aka tafka a ƙarshen makon da ya gabata.

Rahotanni sun bayyana cewa yankin Ƙaramar Hukumar Dala na daga cikin wuraren da ambaliyar ta fi shafa, inda ruwa ya mamaye gidaje da tituna, tare da haddasa cunkoso da asara ga mazauna yankin.

Advertisement

Gwamnatin Kano Ta Fara Horos Da Masu Ɗauko Rahotannin Ayyuka A Ma’aikatu SR /SSR ‎

Mahukunta sun danganta aukuwar ambaliyar da toshewar magudanan ruwa sakamakon tara shara da datti a wuraren da ba su dace ba. Haka kuma, rashin tsaftace magudanan tun kafin damuna na daga cikin dalilan da suka haddasa wannan matsala.

A cewar masana da hukumomin da ke lura da sauyin yanayi, har tun kafin damunar bana, an riga an yi hasashen yiwuwar samun ambaliya a wasu sassa na ƙasar nan, ciki har da jihar Kano. Sai dai da alama ba a dauki matakan kariya da suka kamata ba, lamarin da ya sa ake fuskantar irin wannan bala’i.

Advertisement

Ambaliya irin wannan ta faru a shekarar da ta gabata a Kano, inda ta haddasa asara ga gonaki, shaguna da gidaje, lamarin da ya jefa al’umma da dama cikin mawuyacin hali.

A halin da ake ciki, Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa (NiMET) ta sake fitar da sabon hasashe na yiwuwar samun karin mamakon ruwa a sassa daban-daban na Najeriya daga yau Litinin.

Advertisement

A wasu jihohin arewa kamar Katsina, an ruwaito yadda ambaliya ta riga ta shafi ƙauyuka da dama, inda mutane suka rasa muhallansu kuma yanzu haka suna zama a sansanonin wucin gadi.

Al’ummar da abin ya shafa na roƙon hukumomi da su gaggauta daukar matakan rage radadin bala’in da kuma hana yaduwar matsalar zuwa wasu sassa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending