News
Jami’an Tsaro Sun Bankado Miliyoyin Kuɗi Da Aka Ɓoye A Jaka A Filin Jirgin Sama A Kano
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (EFCC) ta fara bincike kan wani mutum mai suna Ahmad Salisu, wanda Hukumar Kwastam ta kama a Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Mallam Aminu Kano, bisa zargin shigo da kuɗaɗen ƙasashen waje ba tare da bayyana su ba.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya fitar a ranar Litinin a birnin Abuja, jami’an kwastam sun kama Salisu ne yayin wani bincike na tsaro da suka gudanar a filin jirgin, inda suka gano Dalar Amurka $420,900, Fam 5,825 da kuma CFA miliyan 3.95 da CFA 224,000 na ƙasar Kamaru, duk a ɓoye cikin leda da aka lullube da kaya a cikin jaka.
JAMB Ta Ƙayyade Mafi Ƙanƙantar Makin Shiga Jami’a Da Kwaleji
Oyewale ya ce Salisu ya bayyana cewa yana ɗauke da kuɗaɗen ne domin ɗan uwansa, Auwal Ahmad, wanda ke zaune a Saudiyya.
“Ya ce kuɗaɗen na wasu mutum biyu ne, Yusuf Adamu da Abdulhamid Rabiu, waɗanda su ma aka kama lokacin da suka zo domin karɓar kuɗin,” inji sanarwar.
Bayan kammala binciken farko, Hukumar Kwastam ta mika mutanen uku tare da kuɗaɗen da aka kama ga EFCC domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da su a gaban kotu.
Oyewale ya ce “ana shirin gurfanar da su a kotu da zarar an kammala bincike.”
EFCC ta ce wannan kame na cikin jerin matakan da hukumomi ke ɗauka wajen hana safarar kuɗaɗe da kuma yaki da laifukan kudi a tashoshin jiragen saman ƙasar.
