Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Za Ta Kashe Fiye Da Naira Biliyan 69 Don Manyan Ayyuka

Published

on

Gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta amince da kashe fiye da naira biliyan 69 domin gudanar da ayyuka a fannonin ababen more rayuwa, ilimi, lafiya, makamashi da jin ƙai.

Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana haka a wata sanarwa bayan zaman majalisar zartarwa ta jihar karo na 29 da aka gudanar ranar Laraba.

Advertisement

An Kashe Mutum 6,800 Tare Da Sace 5,402 A 2025 A  Najeriya —Rahoto

Daga cikin manyan ayyukan da aka amince da su har da faɗaɗa hanyar Katsina daga Baban Gwari Roundabout zuwa Mil Tara, da gina gada-gadar ƙetare titi guda 5, da aka ware naira biliyan 24.7 domin su.

 

Advertisement

Sauran sun haɗa da gyaran gadar RMK, titin IBB, Kofar Mazugal da hanyar Katsina a kan kuɗi naira 7.8, da kuma ƙarin gada-gadar ƙetare titi guda 10 a wurare masu hatsari, da za su ci biliyan 3.8.

 

Advertisement

A bangaren ilimi, majalisar ta amince da gyaran makarantu 13 da aka rufe a baya da kuma gine-ginen makarantun gwamnati da suka haɗa da kwalejin fasaha ta Dambatta da ta Ungogo da kuɗin da ya kai biliyan 1.2.

 

Advertisement

Hakanan an amince da kafa sabon makarantar firamare a Gishiri-Wuya, Warawa LGA, da gyaran makarantun French da Chinese Bilingual a Kwankwaso da kuɗin da ya kai miliyan 158 da ₦ miliyan 349.

 

Advertisement

Majalisar ta kuma amince da bayar da kuɗaɗe don inganta kula da lafiyar Iyaye da jarirai, allurar rigakafi, da kuma samar da sabon motar Coaster ga Kwalejin Kiwon Lafiya ta Bebeji

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending