Connect with us

News

‎Gwamnatin Kano Ta Ƙaddamar Da Gagarumin Shiri Don Dakile Matsalar Kwacen Waya Da Fadan Daba ‎ ‎

Published

on

satar waya

‎Gwamnatin Jihar Kano ta sake ɗaukar sabon mataki na tunkarar kalubalen tsaro da ke addabar birnin Kano da kewaye, ta hanyar haɗa gwiwa da kungiyoyin farar hula domin magance yawaitar kwacen waya da ayyukan ‘yan daba.

‎Kwamishinan Yaɗa Labarai da Ayyukan Cikin Gida na jihar, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, shi ne ya jagoranci wani taro da aka gudanar domin duba hanyoyin da za a bi don rage aikata laifuka, musamman tsakanin matasa.

Advertisement

Rushewar Gini Yayi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 4 Da Kuma Jikkata 7 A Kano 

‎A cewar Waiya, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya damu matuƙa da yadda rashin tsaro ke ƙara ta’azzara a cikin jihar, musamman ta hanyar kwacen waya da shaye-shaye da suka zama ruwan dare gama gari a wasu unguwanni.

‎”Mai girma Gwamna ya nuna damuwarsa bisa yadda wasu matasa ke afkawa ayyukan daba da tayar da hankali ga al’umma. Wannan ne ya sa gwamnatin sa ke ɗaukar matakin gaggawa domin shawo kan lamarin,” in ji Waiya.

Advertisement

‎Kwamishinan ya bayyana cewa, tun da farko gwamnatin ta kafa wani kwamitin ƙwararru da zai tsara yadda za a shawo kan matsalar cikin tsari da adalci.

‎Kazalika, ya ce an kaddamar da wani shiri mai taken Safe Corridor, wanda ke bai wa matasa da suka tuba daga ayyukan ta’addanci damar samun horo da tallafi domin farfaɗowa daga halin da suka shiga.

Advertisement

“Matasan da suka tuba na ci gaba da samun horarwa da tallafi domin su sake samun damar rayuwa cikin al’umma. Yanzu haka muna aiki da shugabannin ƙananan hukumomi domin samar da tsarin da zai taimaka musu,” a cewarsa.

‎A yayin taron, mahalarta daga sassa daban-daban na kungiyoyin farar hula sun bayyana ra’ayoyinsu da shawarwari. Daya daga cikin mahalarta, Hajiya Rakiya, ta bukaci gwamnati da ta ba masu unguwanni ƙarfi da daraja a ayyukansu.

Advertisement

‎“Masu unguwanni sun fi kowa sanin mazauna unguwanninsu. Idan aka ba su dama da karfi, za su taka rawa matuƙar muhimmanci wajen rage aikata laifuka,” in ji ta.

‎Taron ya ƙare da fatan cewa haɗin gwiwar gwamnati da kungiyoyin farar hula zai kasance wata babbar hanya wajen dakile matsalar daba da kwacen waya a jihar Kano.

Advertisement

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending