Connect with us

News

An Kama Dalibai 11 Da Ake Zargi Kan Kisan Dalibai Biyu A Makarantar Gwamnati A Kano

Published

on

Yan sanda sun cafke wani ango a ranar ɗaurin aurensa kan zargin kisan kai

Rundunar ƴan sanda a Jihar Kano ta tabbatar da cafke mutum 11 da ake zargi da hannu a kisan wasu ɗalibai biyu na makarantar kwana ta Gwamnati da ke garin Bichi, sakamakon wani hari da wasu ɗalibai suka kai bisa zargin luwadi.

Wannan mummunan lamari ya faru ne da misalin ƙarfe 11:30 na daren Litinin, inda wata tawagar ɗalibai suka kai farmaki kan abokan karatunsu huɗu da ake zargin suna aikata luwadi. Harin ya haifar da mutuwar ɗalibai biyu nan take, yayin da sauran biyun suka jikkata matuƙa kuma aka garzaya da su asibitin Bichi domin samun kulawa.

Advertisement

Hauhawar Farashin Kaya Ya Sauka Zuwa Kashi 22.22% a Watan Yuni — NBS

Shaidu daga cikin makarantar sun bayyana cewa, rigimar da aka ɗauka a matsayin fāɗa tsakanin ɗalibai ta rikide zuwa kisan gilla, bayan da aka zargi waɗanda aka kai wa harin da aikata luwadi.

Sunayen waɗanda suka mutu sun kasance Hamza Tofawa da Umar Dungurawa.

Advertisement

A cewar kakakin rundunar ƴan sanda na  jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, an kama mutum 11 da ake zargi da hannu a wannan lamari, kuma tuni aka fara bincike domin gurfanar da su a gaban kotu.

“Ina tabbatar muku da cewa rundunar ƴan sanda ta kama waɗanda ake zargi da hannu a wannan aika-aikar. Ana ci gaba da gudanar da bincike, kuma duk wanda aka samu da laifi ba za a kyale shi ba,” in ji SP Kiyawa.

Advertisement

A martaninsa, Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dr. Ali Haruna Makoda, ta bakin Babban Sakataren Ma’aikatar, Alhaji Bashir Baffa Muhammad, ya bayar da umarnin gudanar da bincike mai zaman kansa domin gano hakikanin abin da ya faru.

“Gwamnati za ta bi duk wata hanya ta gaskiya da adalci domin tabbatar da cewa lamarin bai sake faruwa ba a wani lokaci. Wannan abu abin takaici ne, kuma ba za mu lamunci ɗalibai su ɗauki doka a hannunsu ba,” in ji shi.

Advertisement

Kwamishinan ya kuma mika sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin, yana mai addu’ar Allah ya jikan su da rahama tare da bai wa iyalan haƙurin jure wannan babban rashi.

Haka kuma, Daraktan Hukumar Gudanar da Makarantun Sakandare ta Jihar Kano, Alhaji Abbas Abdullahi, ya bayyana alhininsa kan wannan lamari, yana mai ƙarfafa ɗalibai da su rika amfani da hanyoyin doka wajen warware duk wata matsala.

Advertisement

“Dole ne ɗalibai su rika amfani da hanyoyin doka da tsarin makaranta wajen bayyana korafe-korafensu, maimakon ɗaukar doka a hannu, wanda hakan ke iya janyo asarar rayuka da dukiyoyi,” in ji shi.

Ya kuma ja hankalin iyaye da malamai da su ƙara sa ido a kan ɗabi’u da halayen yara, musamman a cikin makarantun kwana, domin kare lafiyar kwakwalwar matasa da tabbatar da zaman lafiya a cikin al’umma.

Advertisement

 

 

Advertisement

DAILY TRUST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending