News
Yadda Rashin Ruwa Ya Ke Hana Yara Mata Damar Zuwa Makaranta A Shanono
A yayin da duniya ke ci gaba da kokarin ganin yara na samun ilimi, al’ummar ƙauyen Dutsen Bakoshi da ke cikin ƙaramar hukumar Shanono a jihar Kano na fuskantar matsanancin ƙalubale da ke hana yara mata zuwa makaranta – matsalar da ke da nasaba da rashin ruwa mai tsafta.
Rahotanni sun nuna cewa yara mata da dama a yankin sun daina zuwa makaranta saboda ana tura su fita neman ruwa a duk safiya, kafin a kai ga bude aji. Wannan hali ya jima yana jefa iyaye da malamai cikin damuwa da fargabar makomar yaran
Toshewar Magudanar Ruwa Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Matasa 4 A Kano
“Rayuwarmu gaba ɗaya ta koma ruwa. In babu ruwa a gida, to babu komai. Kuma yara mata su ke fita da bokiti kullum don neman ruwa. Wannan na hana su zuwa makaranta,” in ji Malam Musa Isyaku, ɗaya daga cikin dattawan ƙauyen.
A cewar Malama Maryam Tijjani, al’ummar yankin sun shafe shekaru suna amfani da ruwan dam da ba shi da tsafta. “Muna tace ruwan da alum, amma a lokacin rani ruwan kan bushe. A lokacin ne muke shiga mawuyacin hali, saboda ruwa ya fi zinariya tsada,” kamar yadda ta bayyana.
Rahotanni daga yankin sun tabbatar da cewa a lokacin rani, galon ruwa na lita 25 na kai Naira 500. Hakan na nufin gidaje da ke bukatar lita 100 a rana na kashe kusan Naira 2,000 a rana – kimanin N60,000 a wata.
“Ba kowa ke da ƙarfin siyan ruwa ba. Don haka muke tura yara – musamman mata – su fita neman ruwa. Mun fi buƙatar ruwa da abinci fiye da karatu,” a cewar Malama Habiba Tijjani.
Sadiqa Tijjani, yarinya ‘yar shekara 15, ta bayyana cewa ta daina zuwa makaranta tun daga ajin JSS2 saboda kullum sai an tura ta neman ruwa.
“Na yi niyyar karatu, amma kullum sai na fita neman ruwa. Ban da lokacin zuwa makaranta,” in ji ta cikin murya mai rauni.
Sayyada Abdu, ‘yar shekara 16, ta ce ta ajiye karatu tun daga aji na biyar a firamare saboda doguwar tafiyar da ake yi don samo ruwa.
Dagacin ƙauyen, Alhaji Ibrahim Ahmed, ya ce ƙasar yankin na da duwatsu masu tsauri, wanda hakan ke hana ruwa ficewa. “An sha ƙoƙari haƙa rijiyoyi har zuwa zurfin mitoci 200, amma ba a samu ruwa ba,”
Shugaban ƙaramar hukumar Shanono, Hon. Abubakar Barau Shanon, ya bayyana cewa suna tattaunawa da hukumomin da abin ya shafa domin samar da mafita mai dorewa.
“Muna duba hanyar da za ta ba mu damar samar da ruwan sha mai tsafta ga al’umma. Mun fara tuntuɓar hukumomi masu ruwa da tsaki, kuma muna fatan gwamnati za ta ɗauki mataki nan kusa,” in ji shi.
Wata uwa mai yara huɗu, Malama Asma’u Umar, ta ce da zuciya ɗaya suke son yaran su ci gaba da karatu, amma matsin lambar rashin ruwa na hana hakan.
Daya daga cikin shugabannin al’ummar ƙauyen, Malam Saidu Turaki, ya yi kira ga gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu da su taimaka, domin a samu mafita da kuma damar ganin yaran su ci gaba da karatu.
“Ba wai ba mu damu da ilimi ba ne, amma babu ruwa, babu komai. Muna roƙon gwamnati da ta sa mu cikin jerin wuraren da za a kai ayyukan ci gaba na ruwa,” in ji shi.
