Connect with us

News

‎Rashin Gaskiya A Ka Ragal Mulki: EFCC Na Binciken Gwamnoni 18 Masu Ci  ‎ ‎ ‎— Olukoyede

Published

on

gwamnoni

Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (EFCC), Ola Olukoyede, ya ce hukumar na binciken wasu gwamnoni 18 da ke kan mulki a halin yanzu.

‎Ya bayyana hakan ne a wani taron wayar da kai da aka gudanar a Legas, wanda ya hada masu shirya fina-finai da ‘yan canjin kudi domin tattauna matsalolin wulakanta takardun Naira da kuma lalata su.

‎Jami’an Tsaro Sun Cafke Mutum Bisa Mutuwar Yaro Ɗan Shekara Uku A Ramin Kwatar Gidansa

‎Da yake amsa tambaya daga mahalarta taron, Olukoyede ya ce hukumar ba ta jiran sai shugabanni sun gama mulki kafin ta bincike su.

‎“A lokacin da nake magana da ku yanzu, muna binciken gwamnoni 18 da ke kan mulki. Muna fara bincike tun suna ofis, kuma idan sun sauka sai mu shiga mataki na gaba,” in ji shi.

‎Shugaban EFCC ya ce wannan lamari na  almubazzaranci da rashin gaskiya daga wasu shugabanni keyi  hukumar za ta ci gaba da aikinta ba tare da la’akari da matsayin mutum ba.

 

Advertisement

 

KANO TIMES 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending