News
Ganawar Sirri: Kwankwaso ya gana da Shugaba Tinubu a fadar shugaban kasa
Tsohon gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wani taron sirri da aka gudanar a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Rahoton da jaridar Punch ta fitar ya ce taron ya gudana ne a ranar Litinin, jim kadan bayan halartar Kwankwaso a taron Nigeria Forest Economy Summit 2025 da aka gudanar a cikin fadar shugaban kasar.
Gwamnatin Kano Da Kungiyoyin Farar Hula Sun Hada Kai Don Yaki Da Tabarbarewar Tarbiyya Da Laifuka
Wannan dai shi ne karo na biyu da aka bayyana ganawar shugaban kasar da Kwankwaso cikin fiye da shekaru biyu da suka gabata.
A karon farko, sun gana ne a watan Yunin 2023, kwana kalilan bayan rantsar da Shugaba Tinubu, lokacin da Kwankwaso ya kai masa ziyara a matsayin ɗan adawa na farko da ya ziyarci fadar shugaban kasa. A wancan ganawa, Kwankwaso ya bayyana cewa sun tattauna kan batutuwan siyasa da shugabanci tare da nuna yiwuwar yin aiki tare da gwamnatin, kodayake bai bayyana cikakken abin da suka tattauna ba.
A wannan karon kuwa, babu wani bayani daga bangarorin biyu kan abin da suka tattauna a ganawar, kuma fadar shugaban kasa ba ta fitar da wata sanarwa ba.
Taron ya zo ne a daidai lokacin da jam’iyyar adawa ta African Democratic Congress (ADC) ta sanar da kafa wani hadin gwiwa domin kalubalantar jam’iyyar da ke mulki ta All Progressives Congress (APC) a zaben 2027.
Ko da yake jam’iyyar Kwankwaso ta NNPP ba ta cikin wannan sabuwar hadakar da ADC ke jagoranta, rahotanni na nuna cewa akwai kokarin jawo Kwankwaso cikin tafiyar ganin irin karbuwarsa a Arewa da kuma tasirinsa a siyasar Najeriya.
Kwankwaso, wanda ke da shekaru 67, ya taba shugabantar Jihar Kano sau biyu – daga 1999 zuwa 2003 da kuma daga 2011 zuwa 2015. Ya kuma rike mukamin Ministan Tsaro a zamanin Shugaba Olusegun Obasanjo.
A zaben 2023, ya tsaya takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar NNPP inda ya zo na hudu amma ya samu nasara a Jihar Kano da gagarumin rinjaye. Jam’iyyarsa ta kuma lashe kujerar gwamnan jihar da mafi yawan kujerun majalisar dokoki.
Duk da cewa babu wata sanarwa kai tsaye daga bangarorinsu, masana na ganin ganawar zata iya zama wata hanya ta sake tsara dangantaka a tsakanin bangarorin biyu – ko dai wajen janyo Kwankwaso ya mara baya wa gwamnatin Tinubu, ko kuma wani yunkuri daga bangaren Kwankwaso na neman goyon bayan siyasa a zaben 2027.
nzu haka dai ana ci gaba da sa ido kan yadda al’amura za su kaya, musamman ganin irin tasirin da Jihar Kano ke da shi a zaben shugaban kasa a Najeriya.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
