News
Ambaliya Ta Lalata Gidaje Fiye Da 100 A Zakirai
Fiye da gidaje 100 ne suka lalace sakamakon ambaliya a garin Zakirai, da ke ƙaramar hukumar Gabasawa a jihar Kano, bayan ruwan sama mai ƙarfi da aka tafka a yankin.
Ambaliyar ta kuma shafi wani ɓangare na layin dogo da kuma kasuwar garin, inda mazauna suka dora alhakin hakan a kan aikin titin kilomita biyar da ke gudana a yankin, wanda suka ce ba a samar da ingantattun magudanan ruwa ba.
Al’ummar Kofar Kaza A Kano Sun Gudanar Da Sallar Qunut Kan Zargin Wani Hakimi Da Mamaye Filayensu
“Ruwan yana shigowa cikin gidajenmu kai tsaye. Wasu daga cikinmu sun bar gidajensu, wasu kuma na zaune a cikin ruwa. Abincin da muka tanada ya lalace. Muna roƙon agajin gaggawa daga gwamnati da masu hannu da shuni,” in ji Sa’adatu, wata mazauniyar unguwar.
Masana da mazauna yankin sun ce Zakirai ba ta da tarihin ambaliya, sai bayan fara aikin titin .
