News
Jami’an NSCDC Sun Kama Wani Da Ake Zargi Da Dillancin Miyagun Kwayoyi A Kano
Jami’an Hukumar NSCDC a jihar Kano sun kama wasu maza biyu da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi da kuma fasa gidaje.
Mai magana da yawun rundunar NSCDC ta jihar Kano, Ibrahim Abdullahi, ya tabbatar da kama mutanen, inda ya ce an cafke su ne a lokuta daban-daban bisa bayanan sirri da suka samu daga jama’a.
Abdullahi ya bayyana cewa an kama wani da ake kira Ahmed yayin da yake cikin aikata laifin sayar da kuma rarraba haramtattun ƙwayoyi a unguwarsu.
A wani samame daban, jami’an NSCDC sun kuma kama wani saurayi mai suna Muhammad Abbas, mai shekara 22, a unguwar Gurungawa da ke karamar hukumar Kumbotso. Ana zarginsa da fasa gidajen mutane tare da satar kayayyaki masu darajar dubban naira.
Abdullahi ya ce za a gurfanar da dukan waɗanda ake zargi a gaban kotu bayan kammala bincike. Ya kuma yi kira ga jama’a da su cigaba da kasancewa masu lura da yanayi tare da bayar da bayanai masu amfani da za su taimaka wa hukumomin tsaro wajen yaƙi da aikata laifi.
