News
Shugaba Tinubu ya taya dalibai yan Najeriya uku da suka yi fice a Ingilishi da Muhawara da nuna basira a duniya murna
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya matasa uku ‘yan Najeriya murna bisa nasarar da suka samu a gasar TeenEagle Global 2025 da aka gudanar a birnin London na ƙasar Birtaniya, inda suka lashe manyan lambobin yabo a fannoni daban-daban.
Ƴan matan da suka yi zarra a gasar su ne: Nafisa Abdullahi Aminu mai shekaru 17, Rukayya Muhammad Fema mai shekaru 15, da kuma Hadiza Kashim Kalli, wacce ita ma ta nuna bajinta a fagen basira da fasaha.
Gwamnatin Tarayya Ta Yi Hasashen Za A Samu Ambaliya A Wurare 76, Ciki Har Da Kano
A cewar sanarwar da mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan bayanai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a Abuja, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa irin wannan gagarumar nasara alama ce da ke nuna cewar Najeriya cike take da hazikan matasa da za su iya tinkarar kowace irin gasa a matakin duniya.
“Wannan nasarar wata shaida ce ta ingancin tsarin iliminmu da kuma irin baiwar da Allah ya hore wa matasan Najeriya. Hakan ya nuna cewa makomar ƙasar nan za ta yi haske idan muka ci gaba da tallafa wa hazikan yara kamar su,” in ji Tinubu.
An bayyana cewa Nafisa Abdullahi Aminu ce ta lashe matsayi na farko a duniya wajen iya amfani da harshen Turanci, yayin da Rukayya Muhammad Fema ta fi kowa a fagen muhawara. Hadiza Kashim Kalli kuwa ta samu lambar zinariya a matsayin gwanar fasaha da baiwa ta musamman.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da zuba jari a fannin ilimi, musamman ta hanyar Asusun Lamunin Karatu na NELFUND, domin bai wa ɗalibai marasa galihu damar samun damar karatu mai inganci.
Ya kuma ƙara da cewa gwamnati za ta ƙarfafa tsare-tsaren da za su buɗe ƙofofin ci gaba ga matasa da kuma karfafa musu gwiwa wajen ci gaba da himma a karatu da gudanar da ayyukan raya kai da ƙasa.
“Ina roƙon Nafisa, Rukayya da Hadiza da su ci gaba da dagewa a karatunsu tare da zama jakadu na gari ga Najeriya a idon duniya. Muna alfahari da su, kuma muna fatan karin nasarori a rayuwarsu,” in ji Shugaban Ƙasa.
Lamarin ya ja hankalin jama’a da dama a cikin gida da waje, inda aka bayyana matasan a matsayin ƙwararru da suka dace da yabo da tallafi daga kowanne mataki na gwamnati da al’umma.
