News
Gwamnatin Tarayya Ta Yi Hasashen Za A Samu Ambaliya A Wurare 76, Ciki Har Da Kano
Gwamnatin Tarayya ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama mai yawa daga ranar 5 zuwa 9 ga watan Agusta, wanda zai iya haddasa ambaliya a jihohi 19 da kuma ƙauyuka da birane 76 a faɗin ƙasar nan.
Cibiyar Gargaɗin Ambaliya ta Ƙasa ce (National Flood Early Warning Systems Centre) ƙarƙashin Ma’aikatar Muhalli ta bayyana haka a ranar Talata, inda ta bukaci hukumomi da al’umma su ɗauki matakan kariya.
Kwamishinan Sufuri Yayi Murabus Bayan Cece-kuce Akan Belin Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi
Hasashen ya zo ne a daidai lokacin da wasu sassan jihohin Ogun da Gombe ke fuskantar ambaliya, yayin da jihohin Legas, Filato, Anambra da Delta suma suka fuskanci tasirin ruwan sama mai yawa.
Kano na daga cikin wuraren da ke cikin haɗarin ambaliya a cikin rahoton, an bayyana wasu garuruwa da ke cikin haɗarin ambaliya, inda aka ce.
A jihar Kano: Bebeji, Gezawa, Gwarzo, Birnin Kano, Karaye, Tundun Wada, Wudil da Kunchi.
A Kebbi: Bagudo, Birnin-Kebbi, Bunza, Gwandu, Jega, Kalgo, Kamba, Kangiwa, Shanga, Ribah, Sakaba, Saminaka, Yelwa da Gauri-Banza.
A Bauchi: Tafawa-Balewa, Azare, Jama’are, Kari, Misau da Jama’a.
A Benue: Agaku, Buruku, Gboko, Igumale, Ito, Katsina-Ala, Ugba da Vande-Ikya.
A Kaduna: Jaji, Kafanchan, Birnin Gwari da Zaria.
A Katsina: Bindawa, Bakori, Daura da Funtua.
A Nasarawa: Keana, Keffi da Wamba.
A Jigawa: Diginsa, Gumel, Dutse, Gwaram, Hadejia da Miga.
A Ebonyi: Abakaliki, Echara da Ezilo.
A Cross River: Ogoja Edor da Obubra.
A Akwa Ibom: Edor, Eket, Ikom, Oron da Upenekang.
A Sokoto: Sokoto da Wamakko.
A Zamfara: Anka.
A Yobe: Machina da Potiskum.
A Borno: Biu.
A Gombe: Bajoga.
A Niger: Kontagora, Rijau da Ringim.
A Plateau: Mangu.
A Taraba: Donga da Takum.
-
News22 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
