Connect with us

News

NAHCON Ta Sanar Da Naira Miliyan 8.5 A Matsayin Kuɗin Ajiya Na Aikin Hajjin 2026

Published

on

Hajjin ban

Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta bayyana cewa ta tsayar da naira miliyan 8.5 a matsayin kuɗin ajiya na farko ga maniyyatan Hajjin shekarar 2026.

Wannan mataki na daga cikin shirye-shiryen farko da hukumar ke ɗauka domin farawa da wuri wajen tsara yadda za a gudanar da aikin Hajji na shekara mai zuwa, wanda ake sa ran zai gudana cikin watan Mayu ko Yuni na 2026, bisa ga jadawalin da Saudiyya ta fitar tun a watan Yuli.

Advertisement

Ƴan Sanda Sun Gano Bama-Bamai Da Makamai a Cikin Kayan Bola a Kaduna

A wata sanarwa da hukumar ta fitar bayan wani taro da ta yi da shugabanni da sakatarorin hukumomin jin dadin alhazai na jihohin Najeriya a ranar Alhamis, NAHCON ta bayyana cewa wannan tsayayyen farashi ba shine na ƙarshe ba, illa dai a matsayin “farashi na ajiya” da zai buɗe kofar shiri ga maniyyata da hukumomi.

Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya ce matakin zai ba wa mutane damar fara tanadi da kuma bai wa gwamnati da hukumomin jihohi damar fara shirye-shiryen cikin lokaci.

Advertisement

“Kuɗin miliyan 8.5 da muka kayyade shi ne farashi na farko, ba shine na ƙarshe ba. Har yanzu tattaunawa da ƙididdiga na ci gaba tsakanin NAHCON da hukumomin Saudiyya da sauran masu ruwa da tsaki,” in ji shi.

Farfesa Saleh ya kuma bayyana cewa Saudiyya ta sake ware wa Najeriya kujeru 95,000 kamar yadda ta yi a bara, lamarin da ya nuna babu canji dangane da yawan masu aikin Hajji da ake sa ran karɓa daga Najeriya a shekarar 2026.

Advertisement

A cewar NAHCON, wannan tsari na fara shiri tun da wuri zai taimaka wajen kauce wa matsalolin lokaci da rashin daidaituwa da suka saba shafar shirye-shiryen Hajji, musamman idan an jira karshe kafin a fara tsare-tsare.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending