News
Gwamnatin Kano Ta Bayar Da Kwangilar Hanyoyi 17 Akan Sama Da Naira Biliyan 40
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana a ranar Talata cewa, ta bayar da kwangilar gina tituna acikin birnin Kano guda 17 a kan kudi sama da Naira biliyan 40.8.
Titunan ana aikinsu ne a kananan hukumomin Gwale, Nasarawa, Kumbotso, Fagge, Kano Municipal, Tarauni, Dala, da Ungogo.
Kwamishinan yada labarai, Ibrahim Waiya ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke rangadi da shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa, a titunan da aka kammala da wadanda kuma ake kan aikinsu.
Ya ce daga cikin ayyukan akwai Tudun-Yola–Gwarzo Road da Dansudau Bypass (N1.896bn), Jafar–Madobi Road da underpass (N1.323bn), Sabo Bakin Zuwo Road (N2.014bn), da kuma Muhammad Buhari Road (N4.108bn).
Sauran sun haɗa da Rijiyar Lemo Road (N494.3m), aikin magance zaizayar ƙasa a Kwanar Durba–Fammar-Kunau Kure Road (N205.9m), da gyaran Airport Road (N5.956bn).
Ya ƙara da cewa gwamnati na kashe N13.3bn wajen aikin hanyar Rogo–Bari–Falgore–Mahangi a Rogo LGA, da kuma N6.9bn wajen aikin hanyar Panda–Hamdullahi–Albasu–Salkwayan Dutse a Albasu LGA.
Waiya ya ce, kwangilolin sun nuna aniyar Gwamna Abba Yusuf na samar da ababen more rayuwa musamman tituna, wanda ya bayyana a matsayin jigon alkawarin da ya yi a yayin yakin neman zabe.
A cewar kwamishinan, ayyukan na da nufin inganta hanyoyin zirga-zirga, da rage cunkoson ababen hawa, da inganta rayuwar al’ummar jihar baki daya.
