Connect with us

News

Fursunoni 16 Sun Tsere Daga Gidan Yari A Nasarawa

Published

on

Kotu ta yanke wa Muhammad Buba hukuncin daurin rai da rai bisa laifin kashe mahaifinsa

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Kasa (NCoS) ta tabbatar da cewa fursunoni 16 sun tsere daga Gidan Gyaran Hali da ke Keffi, jihar Nasarawa, da safiyar Talata.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Abubakar Umar, ya ce wasu daga cikin fursunonin sun karya duk matakan tsaron wurin, suka kai wa jami’an da ke aiki hari, lamarin da ya ba su damar tserewa.

Jami’an Hukumar EFCC Sun Tsare Aminu Waziri Tambuwal, Tsohon Gwamnan Sokoto 

Jami’ai biyar sun ji rauni, biyu daga cikinsu na cikin halin gaggawa a asibitin gwamnati.

Ya bayyana cewa an kama fursunoni bakwai daga cikin wadanda suka tsere, yayin da ake cigaba da neman sauran tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro.

Shugaban hukumar, Sylvester Nwakuche, ya ziyarci wurin, inda ya umarci a gudanar da bincike mai zurfi.

Ya gargadi cewa duk jami’in da aka samu da hannu ba zai tsira daga hukunci ba.

Advertisement

Hukumar ta roki jama’a da su kasance cikin natsuwa, su rika lura, tare da sanar da hukumomin tsaro idan sun ga ko sun ji labarin duk wani daga cikin wadanda suka tsere.

 

 

 

WIKKI TIMES 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending