News
Allah Ya Yi Wa Sarkin Zuru, Muhammadu Sani Sami Rasuwa Yana Da Shekaru 81 A Duniya
Allah Ya yi wa Sarkin Zuru a Jihar Kebbi, Mai Martaba Alhaji Muhammadu Sani Sami (Gomo II), rasuwa da safiyar Lahadi a wani asibiti da ke birnin Landan, bayan gajeriyar jinya.
Marigayin, wanda tsohon babban jami’in soja ne, ya rasu yana da shekaru 81 a duniya.
Shugabannin Siyasa Ne Ke Hura Wutar Fadan Daba A Kano — Barista Abba Hikima
An haifi Muhammadu Sani Sami a ranar 24 ga Oktoba, 1943. Ya shiga rundunar sojin Nijeriya a ranar 10 ga Disamba, 1962, inda ya yi horo a Mons Officer Cadet School da ke Aldershot, Birtaniya. A ranar 25 ga Yuli, 1963 aka ba shi sarauta ta soja tare da abokan horo da suka haɗa da tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida.
A cikin harkar soja, marigayin ya riƙe manyan mukamai masu muhimmanci. A zamanin Janar Murtala Ramat Mohammed, ya shugabanci Brigade of Guards a Legas. Daga bisani, bayan juyin mulkin 1983 da ya kawo Janar Muhammadu Buhari kan mulki, aka naɗa shi gwamnan soja na Jihar Bauchi, mukamin da ya riƙe daga watan Disamba 1983 zuwa Agusta 1985.
Bayan ya yi ritaya daga rundunar soja, Muhammadu Sani Sami ya koma ƙauyensa, inda daga bisani aka naɗa shi Sarkin Zuru. A matsayin sa na sarki, ya shahara da kishin ci gaban al’umma, sauƙin kai, da jajircewa wajen kare al’adun gargajiya.
Rasuwar Sarkin ta bar babban gibi a masarautar Zuru da kuma Jihar Kebbi baki ɗaya, inda ake ganin shi a matsayin jagora mai kishin ƙasa da kishin al’umma.
