Connect with us

News

Jami’an ’Yan Sanda Sun Cafke Mutum Biyu Da Ake Zargi Da Sata, Sun Kwato Wayoyi 23, Na’urorin POS A Kano 

Published

on

Yan sanda sun cafke wani ango a ranar ɗaurin aurensa kan zargin kisan kai

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta kama wasu matasa biyu da ake zargi da sata, tare da kwato kayayyaki masu yawa da suka haɗa da wayoyin hannu 23, na’urorin POS, da katunan banki.

Wadanda aka kama su ne Umar Aliyu, mai shekara 25, da Sabiu Kabiru, mai shekara 27, dukkansu mazauna Gunduwawa a Karamar Hukumar Gezawa. Jami’an rundunar ta musamman Special Intervention Squad (SIS) ne suka cafke su a ranar 7 ga Agusta, 2025 da misalin ƙarfe 3:00 na rana, bayan samun sahihin bayanan sirri da umarnin Kwamishinan ’Yan Sanda na Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori.

Advertisement

Rashin Adalci Ne A Sanya Juma’a A Matsayin Ranar Aiki Ga Musulmi A Najeriya —Reno Omokri

Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa an kwato:

Wayoyin hannu guda 23 (Android 10, Keypad 13),Na’urorin POS guda 3 ,Katunan Opay guda 17, MP3 guda 3, Batirin waya guda 8, Power bank guda 1

Advertisement

Binciken farko ya nuna cewa wadanda ake zargin sun shiga wata cibiyar kasuwanci a Karamar Hukumar Takai, inda suka yi satar kayayyakin. Sai dai rundunar ta ce ta gano wasu rashin daidaito a bayanan da suka bayar, kuma ta umarci a nuna kayayyakin a hedikwatar rundunar da ke Bompai, domin masu su zo su tantance.

Kwamishinan ’Yan Sanda na Kano, CP Bakori, ya yabawa jami’an rundunar bisa jajircewa da kwarewa a gudanar da bincike, tare da jaddada aniyar hukumar wajen ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a jihar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending