Connect with us

News

Gwamnan Kano Zai Kaddamar Da  Majalisar Shurah

Published

on

Gwamnatin jihar Kano za ta kaddamar da sabuwar Majalisar Shurah a ranar Litinin, 8 ga watan Satumba, 2025, karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabiru Yusuf.

Bikin kaddamarwar zai gudana ne a fadar gwamnatin jihar da ke Kano, kamar yadda sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Malam Ibrahim Abdullahi Waiya, ya fitar a ranar Talata ta bayyana.

Advertisement

Jami’an NSCDC Sun Kama Mutane 6 Da Ake Zargin Barayin Wayoyin Wutar Lantarki Ne A Kano

Majalisar za ta kasance wata kafa ta bayar da shawara ga gwamnatin jihar, tare da taimaka mata wajen aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da ake sa ran za su kawo ci gaba mai dorewa a Kano.

 

Advertisement

A cewar gwamnatin jihar, an kafa majalisar ne domin karfafa hadin kai, tabbatar da gaskiya da adalci wajen yanke shawara, da kuma samar da daidaito a wakilcin mazabu daban-daban.

Majalisar za ta kunshi fitattun mutane daga sassa daban-daban na jihar, wadanda ake ganin za su taka muhimmiyar rawa wajen ganin Kano ta samu ci gaba.

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending