News
Ambaliyar Ruwan Sama Ta Halaka Mutane 231 Ta Jikkata Wasu 607 A Najeriya
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta bayyana cewa akalla mutane 231 sun rasa rayukansu, yayin da wasu 114 ke bata sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye sassa daban-daban na Najeriya a shekarar 2025.
Binciken hukumar ya kuma nuna cewa mutane 607 sun jikkata, yayin da sama da 315,762 aka ruwaito cewa Ambaliyar ta shafa daga aƙalla jihohi 25 da kananan hukumomi 86. Daga cikinsu, 113,367 aka tilasta musu barin gidajensu. Haka kuma, gidaje 40,493 sun rushe, yayin da gonaki 46,304 suka nutse cikin ruwa.
Kungiyoyin Farar Hula 201 a Kano Sun Yi Watsi da Zanga-zangar Siyasa Kan Cin Hanci
Masana sun danganta wannan mummunar masifa da ruwan sama mai tsanani, ƙarancin tsarin magudanan ruwa, da kuma sakin ruwa daga manyan dam-dam. Sun ƙara da cewa sauyin yanayi ya ƙara tsananta matsalar.
Rahotanni sun nuna cewa yara da mata sune mafiya shan wahala daga ambaliyar. Yara 143,683 sun kamu da illa, yayin da mata 100,079 aka ruwaito sun shiga cikin waɗanda abin ya shafa. Haka kuma, tsofaffi 11,592 da masu nakasa 2,265 sun shiga cikin waɗanda ambaliyar ta rutsa da su.
A jerin jihohin da suka fi fuskantar Ambaliyar, Legas ta fi yawan mutane da abin ya shafa da 52,013, sai Adamawa da 51,713, da kuma Akwa Ibom da 46,233. A Arewa maso Gabas kuwa, Borno ta samu 8,164, yayin da Kaduna ta ruwaito 7,334. Bisa rarrabuwa ta yanki, Kudu maso Kudu ya fi shan wahala da mutane fiye da 101,000 da abin ya shafa, inda sama da 61,000 aka tilasta musu barin gidajensu.
Gwamnatin Tarayya ta sake fitar da gargadin sabuwar ambaliya, inda ta lissafa jihohi 17 da za su iya fuskantar ruwan sama mai nauyi tsakanin 6 zuwa 8 ga watan Satumba, 2025. Jihohin sun haɗa da Kebbi, Katsina, Kano, Bauchi, Nasarawa, Adamawa, Gombe, Filato, Anambra, Imo, Kogi, Sokoto, Kaduna, Akwa Ibom, Rivers, Delta da Benue.
