News
Kotun Ghana Ta Yanke Wa ’Yan Najeriya 3 Hukuncin Ɗaurin Shekaru 96 Saboda Satar Mota
Wata kotu da ke ƙasar Ghana ta yanke wa ’yan Najeriya uku hukuncin ɗaurin shekaru 96, bayan samun su da laifin satar mota a birnin Kumasi na ƙasar.
Kotun dai ta samu Francis Friday da Linus Agwazie da kuma Russell Ekenze ne da laifin a daidai lokacin da ’yan ƙasar ke neman a kori ’yan Najeriya daga kasar saboda aikata laifuka.
Shettima Ya Yabawa Uba Sani Kan Kafa Majalisar Kwarewa Ta Jihar Kaduna
Mai magana da yawun ’yan sandan yankin Ashanti na ƙasar, Godwin Ahianyo, ne ya bayyana yanke hukuncin a cikin wata sanarwa ranar Talata.
Sanarwar ta ce an kama mutanen ne ranar 20 ga watan Yuni bayan an zarge su da satar wasu motoci da ke ajiye.
Godwin ya ce bayan kama su ne aka gurfanar da su a gaban kotun a ranar 22 ga watan Yuli a gaban kotun da ke Atasemanso, kan zargin satar motar.
A ’yan watannin nan dai ana samun rahotannin ƙaruwar ’yan Najeriya da ke aikata laifuka a ƙasar ta Ghana.
Ko a watan Mayu, sai da wata kotun kasar da ke Tarkwa ta yanke wa wata ’yar Najeriya hukuncin ɗaurin shekara 20, bayan samun ta da laifin safarar ’yan mata huɗu tare da shigar da su karuwanci a ƙasar.
Kazalika, a watan Yuli, Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasar ta kama ’yan Najeriya 50 bisa zargin aikata zamba ta intanet da kuma safarar mutane.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
