Connect with us

News

Cizon Macizai Ya Lakume Rayukan Mutane 23, Sama Da 1,800 Sun Samu Rauni A Gombe — Rahoto

Published

on

images 13

Rahotanni sun nuna cewa jihar Gombe ce ta fi kowace jiha fama da yawaitar cizon macizai a Najeriya, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 23 da kuma raunata sama da 1,800 cikin watanni bakwai kacal.

Shugaban kwamitin gaggawa na kasa kan cizon macizai, Dr. Isma’il Jibrin, ne ya bayyana hakan a yayin taron shekara na biyu na Toxicology Society of Nigeria (TSN) da aka gudanar a Gombe. Taron ya gudana ne kan taken: “Bincike kan Samar da Maganin Cizon Macizai a Najeriya.”

Cizon Macizai Ya Lakume Rayukan Mutane 23, Sama Da 1,800 Sun Samu Rauni A Gombe — Rahoto

A cewar bayanan da aka tattara daga Cibiyar Bincike da Maganin Cizon Macizai da ke Kaltungo, tsakanin watan Janairu zuwa Yuli na shekarar 2025 an samu cizon maciji 1,829, inda mutum 23 suka mutu.

Dr. Isma’il ya ce sama da kashi 75 cikin 100 na wadanda ake cizon maciji a Najeriya maza ne, yayin da ya bayyana cewa carpet viper ita ce maciji mafi hatsari a kasar.

Sai dai ya nuna damuwa kan tsadar maganin cizon maciji, duk da cewa Najeriya na da izini daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) na samar da maganin domin amfani a cikin gida.

A nasa bangaren, shugaban kwamitin amintattu na TSN, Dr. Ibrahim Jalo Daudu, ya ce an zabi jihar Gombe domin taron ne saboda ita ce ta fi fama da cizon maciji a fadin kasar.

Advertisement

Ya bukaci gwamnati da masu ruwa da tsaki da su kara zuba jari wajen samar da magungunan cikin gida, domin rage tsada da kuma rage dogaro da kasashen waje.

 

BIZPOINT

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending