Connect with us

News

Da Dumi-Dumi: Shugaba  Tinubu ya sanar da kawo karshen dokar ta-baci a Jihar Ribas

Published

on

FB IMG 1755800862838

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cewa dokar ta-baci da ya ayyana a Jihar Ribas ta ƙare, kuma ba za a tsawaita ta ba.

Tinubu ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar daga fadar shugaban ƙasa a yau Laraba, 17 ga Satumba, 2025.

Advertisement

Da Dumi-Dumi: Ba zan tsawaita dokar ta bacin da na sanya a jihar Rivers ba – Shugaba Tinubu

Ya tunatar da cewa an ayyana dokar ta-bacin ne a ranar 18 ga Maris, 2025, sakamakon rikicin siyasa da ya durƙushe harkokin gwamnati a Ribas.

A cewar shugaban ƙasa, rikicin ya samo asali ne daga rashin jituwa tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da Majalisar Dokokin jihar, inda aka rarrabu gida biyu – wasu huɗu na tare da gwamna, yayin da sauran 27 suka tsaya kan kakakin majalisar, Martins Amaewhule.

Advertisement

Tinubu ya ce wannan rabuwar kawunan ya jefa jihar cikin rikicin mulki, wanda har kotun koli ta tabbatar da cewa babu ingantacciyar gwamnati a Ribas a lokacin.

Sai dai a cewar shugaban ƙasa, cikin watanni shida da dokar ta-bacin ta ɗauka, an samu sabon yanayi na fahimtar juna tsakanin ɓangarorin siyasar jihar.

Advertisement

Ya ce daga ranar Alhamis, 18 ga Satumba, 2025, gwamna, mataimakiyarsa, da ‘yan majalisar dokokin jihar za su koma bakin

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending