Connect with us

News

Stallion Times Ta Mika Sakon Ta’aziyya Bisa Rasuwar Sarkin Gabas, Idris Adamu Dankabo

Published

on

IMG 20250919 WA0005

Jaridar Stallion Times ta bayyana alhini da jimami kan rasuwar Sarkin Gabas, Idris Adamu Dankabo, wanda ya rasu a hatsarin mota yana da shekaru 48 a duniya a ranar Alhamis.

A cikin wata sanarwa da Babban Editan Stallion Times, Isiyaku Ahmed, ya fitar a ranar Juma’a, ya bayyana marigayin a matsayin jagoran gargajiya mai kishin al’umma, kuma aboki na hakika ga jaridar.

Advertisement

Masar Ta Gano Ɓarayin Munduwar Fir’auna Da Suka Narka Tare Da Sayar Da Ita

Sanarwar ta ce marigayin Dankabo mutum ne mai tsoron Allah, wanda rayuwarsa ta kasance ta gaskiya da rikon amana da kuma hidima ga jama’a.

“Ya kasance mutum mai mu’amala da kowa, ba tare da bambanci na addini ba, ko matsayi, ko asalinsa. Wannan hali nasa ya sa ya samu soyayya da girmamawa daga kowane ɓangare,” in ji sanarwar.

Advertisement

Jaridar ta kuma mika ta’aziyya ga iyalansa, Majalisar Masarautar Kano, abokai, masoya da daukacin al’ummar Kano bisa wannan babban rashi da ya faru.

“Muna roƙon Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta masa, Ya yi masa rahama, Ya sanya shi cikin Aljannatul Firdaus, sannan Ya ba wa iyalansa da masoyansa hakuri da juriyar wannan rashi,” a cewar sanarwar.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending