News
Samar Da Yan Sandan Jiha, Hanyar Haddasa A Fitina Ce – Tsohon AIG
Wani tsohon babban jami’in ƴan sanda da ya taɓa zama Kwamishinan ƴan sanda a jihohin Oyo, Sokoto, Kebbi da Imo, kuma ya jagoranci makarantar horar da ƴan sanda ta ƙasa da ke Kano, ya bayyana cewa mafita ita ce a inganta kuɗaɗen aiki da kuma yin garambawul ga tsarin ƴan sanda na tarayya da ake da shi tare da rungumar tsarin tsaron al’umma.
Bolanta, wanda ya bayyana irin gogewarsa wajen kula da tsaro a jihohin da ke fama da rikice-rikice, ya yi tambaya kan manufar waɗanda ke fafutukar ganin an kafa ƴan sandan jiha.
Ya yi watsi da iƙirarin cewa gwamnatocin jihohi sun fi ƙwarewa wajen ɗaukar nauyin rundunar ƴan sanda, yana mai nuna cewa akwai wasu jihohi da ba za su iya tsayawa da ƙafafunsu ba sai da tallafin gwamnatin tarayya, har ma suna ta fama wajen biyan albashin ma’aikatansu.
A cewarsa, bai dace a ɗora irin waɗannan jihohi da nauyin kula da rundunar tsaro mai rikitarwa irin ta NPF ba. Ya kuma nuna cewa sama da kashi 70 na ƴan sanda a yawancin jihohi ƴan asalin wuraren ne, don haka wakilci na gari ba shi ne babbar matsalar tsaron Najeriya ba.
Maimakon ƙirƙirar wani sabon tsari na ƴan sanda, tsohon AIG ɗin ya buƙaci a koma kan ginshikan asali na inganta kuɗaɗe da kayan aiki ga rundunar ƴan sanda ta ƙasa.
