Connect with us

News

Akalla Mutane 4,778 Ne Suka Mutu Sakamakon Cutar Kwalara A Najeriya  — Rahoto 

Published

on

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta bayyana cewa akalla mutane 4,778 ne suka mutu sakamakon cutar kwalara tsakanin shekarar 2020 zuwa 2024 a faɗin ƙasar.

Rahoton hukumar ya nuna cewa a shekarar 2020 an samu mutane 3,513 da ake zargin sun kamu da cutar, inda mutane 95 suka mutu. Sai dai, adadin ya ƙaru matuƙa a 2021, inda aka samu mutane 111,062 da ake zargin sun kamu da cutar, kuma 3,604 daga cikinsu suka mutu a jihohi 33 na ƙasar.

Advertisement

Fiye Da Kashi 35 Na Yaran Nijeriya Na Fama Da Rashin Abinci Mai Gina Jiki – Ƙungiyar Likitoci

A shekarar 2025 kaɗai, fiye da mutane 300 ne suka mutu sakamakon barkewar cutar, ciki har da mutane 179 da gwamnatin Zamfara ta tabbatar sun rasu daga cikin 12,052 da ake zargin sun kamu da cutar a watan Satumba.

 

Advertisement

A jihar Bauchi, mataimakin gwamnan jihar, Auwal Mohammed Jatau, ya bayyana cewa mutane 58 ne suka mutu daga cikin 258 da ake zargin sabbin kamuwa da cutar a ƙananan hukumomi 14 na jihar. Wannan bayani ya fito ne makonni biyu da suka gabata, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Wannan al’amari na faruwa ne duk da miliyoyin dalolin da Najeriya ta karɓa a matsayin bashi daga Babban Bankin Duniya domin samar da ruwa mai tsafta da muhalli mai inganci, da kuma tallafin dala miliyan biyu daga Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) don samar da rigakafin cutar kwalara.

Advertisement

Masana sun ce yadda cutar ke ƙaruwa duk shekara duk da wadannan tallafe-tallafe na nuna ƙalubalen da ake fuskanta wajen samar da ruwa mai tsafta, tsaftar muhalli da ingantaccen tsarin kiwon lafiya, musamman a yankuna

n karkara.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending