News
Shugabannin Kafofin Yada Labarai A Kano Sun Bukaci Jama’a Su Yi Rijistar Katin Zabe
Shuwagabannin kafofin yada labarai na Kano (Heads of Media Forum) sun bukaci al’umma da su tabbatar sun yi rijistar katin zabe, don inganta dimokuradiyya.
Shugaban kungiyar, Ado Sa’idu Warawa, ya yi wannan kiran ne a taron manema labarai da aka gudanar a Kano ranar Asabar. Ya ce yin rajistar katin zabe ginshiki ne na tabbatar da sahihancin zabe.
Fiye da ‘Yan Mata 2,200 Suka Fuskanci Cin Zarafi A Cikin Shekara Ɗaya A Legas — Rahoto
Warawa ya gargadi jama’a da kada su jira zuwa lokacin zabe kafin su sabunta katin su, ya kuma bukaci kowa da kowa ya ziyarci wuraren rajista, ya bi ka’idojin da aka tsara.
Ya kuma bukaci a yi amfani da kafafen yada labarai da kungiyoyin matasa wajen wayar da kan jama’a game da rajistar katin zabe, musamman ta yanar gizo.
Bugu da kari, Warawa ya yaba da ci gaban da gwamnati ke sanarwa wajen gina asibitoci, makarantu da Ababen more Rayuwa a fadin jihar.
-
News1 day ago
Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano
-
News3 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
