News
Cutar Lassa Ta Yi Ajalin Mutum 172 A Bana A Najeriya— Hukumar NCDC
Hukumar da ke yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta tabbatar da alƙaluman mutane 172 a matsayin waɗanda zazzaɓin Lassa da ɓera ke yaɗawa ya hallaka a sassan ƙasar cikin shekarar da muke ta 2025.
Sabon rahoton da hukumar ta fitar ya nuna cewa jumullar mutum 924 aka tabbatar sun kamu da cutar ta Lassa a sassan Najeriya cikin shekarar nan.
Fashewar Tankar Mai A Neja Ya Lakume Rayukan Mutum 39, Ya Jikkata Sama Da 60 – NEMA
Alƙaluman da ke wakiltar makwanni 40 na wannan shekarar, ya nuna cewa an samu adadin masu ɗauke da cutar ne daga ƙananan hukumomi 106 cikin jihohin ƙasar 21.
Rahoton na NCDC ya nuna cewa haɗarin mutuwa sakamakon wannan cuta ta Lassa na a matakin kashi 18.6 cikin 100 daga kashi 17 da ake gani a irin wannan lokaci cikin shekarar da ta gabata ta 2024.
NCDC ta ce kashi 90 na masu ɗauke da wannan cuta sun fito ne daga jihohi 5 da suka ƙunshi jihar Ondo mai kashi 35 da Bauchi mai kashi 22 kana Edo da kashi 17 tukuna jihar Taraba da kashi 13 sai kuma Ebonyi mai kashi 3.
Rahoton na NCDC ya ce sauran jihohin Najeriyar 16 su ke da kashi 10 na masu ɗauke da cutar ta Lassa.
Hukumar ta NCDC ta ce galibi masu cutar mutane ne da shekarunsu ya fara daga 21 zuwa 30, kuma galibi maza suka fi kamuwa.
-
News1 day ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News17 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
