News
Fashewar Tankar Mai A Neja Ya Lakume Rayukan Mutum 39, Ya Jikkata Sama Da 60 – NEMA
Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta tabbatar da cewa aƙalla mutane 39 sun mutu, yayin da sama da 60 suka jikkata sakamakon fashewar tankar mai a jihar Neja.
Lamarin ya faru ne a ranar Talata a ƙauyen Essa, da ke kan hanyar Agaie–Bida a ƙaramar hukumar Katcha, bayan da wata tankar mai ta kife ta kuma kama da wuta. Rahotanni sun bayyana cewa wasu mazauna yankin sun taru suna ƙoƙarin dibar mai daga cikin tankar da ta kife kafin ta fashe.
Ma’aikatar Muhalli Ta Dakatar da Rangwamen Izini Ga Masana’antu A Kano
Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago, ya bayyana jimaminsa game da wannan mummunan lamari, yana mai cewa abin takaici ne yadda jama’a ke cigaba da taruwa a kusa da tankar da ta kife domin dibar mai, duk da wayar da kai da aka yi a kan hatsarin da ke tattare da hakan.
-
News1 day ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News17 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
