Connect with us

News

Gobara Ta Ƙone Rumfuna Sama Da 500 A Kano

Published

on

IMG 20251023 WA0015

Rahotanni daga jihar Kano na cewa, gobara ta tashi a kasuwar Shuwaki da ke cikin ƙaramar hukumar Gari, inda ta ƙone rumfuna sama da 500 kurmus.

Mai magana da yawun Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano, ACFO Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin a wani jawabi da ya fitar, inda ya ce wutar ta tashi ne da misalin ƙarfe 3:25 na rana a ranar Laraba.

Advertisement

Hare-haren ’Yan Bindiga Ya Fara Ƙamari A  Yankin  Shanono, Jihar Kano

A cewar Abdullahi, hukumar ta samu kiran gaggawa daga kwamandan Hukumar na Gari, Abdulmalik Muhammad, wanda ya sanar da tashin wutar.

Ya ce, “Daga nan ne tawagar jami’an Hukumar daga ofishin Danbatta suka isa wurin don kashe wutar. Da isarsu, sun tarar da kasuwar — wacce ke da fadin kusan kafa 3,000 zuwa 2,500 da rumfuna fiye da 1,000 — tana ci da wuta. Akalla rumfuna 529 ne suka ƙone gaba ɗaya.”

Advertisement

Sai dai babu rahoton asarar rai a lamarin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending