Connect with us

News

Dakarun Soji Sun Yi Nasarar Kashe Ƴan Ta’adda Sama Da 50 a Borno Da Yobe

Published

on

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 101 Sun Kama Wasu 182 A Cikin Mako Daya

Hedikwatar tsaron Najeriya ta ce dakarun Operation Hadin Kai sun kashe sama da ƴan ta’adda 50 tare da dakile hare-hare a sansanonin sojoji a jihohin Borno da Yobe.

Rundunar sojin ta ce mayakan sun kai hare-hare a lokaci guda daga daren Alhamis har zuwa wayewar gari, inda suka farmaki sansanonin sojoji a Dikwa, Mafa, Gajibo da Katarko, waɗanda ke ƙarƙashin sassan 1 da 2 na rundunar hadin gwiwa ta 1.

Advertisement

Gobara Ta Ƙone Rumfuna Sama Da 500 A Kano

A wata sanarwa, jami’in yada labarai na rundunar hadin gwiwa ta Arewa maso Gabas (OPHK), Lt.-Col. Sani Uba, ya ce sojojin sun yi namijin ƙoƙari wajen dakile hare-haren mayakan, inda suka yi wa ƴan ta’adda mummunar asara.

Uba ya ce rundunar ta samu nasarar kashe sama da ƴan ta’adda 50, tare da kwato makamai da dama ciki har da bindigogi AK-47 guda 38, PKT guda 7, makamin RPG guda 5, gurneti da tarin albarusai.

Advertisement

Kafin wannan sanarwa, wasu majiyoyin tsaro sun tabbatar wa jaridar Premium Times cewa sojoji na fafatawa da mayakan ISWAP a garuruwan Mafa da Dikwa, inda aka samu asarar rayuka a bangarorin biyu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending