News
Hisbah Ta Tarwatsa Taron Da Ake Zargi Da Auren Jinsi A Kano
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta tarwatsa wani taron da ake zargin ya shafi auren jinsi a wani dakin taro da ke unguwar Hotoro By-pass a cikin birnin Kano, a ranar Asabar, 25 ga Oktoba, 2025.
Rahotanni sun ce taron, wanda aka gudanar a Fatima Event Center, ya jawo hankalin jami’an Hisbah bayan samun bayanan sirri daga wasu mazauna yankin.
Ƴan Bindiga Sun Budewa Mota Dauke Da Fasinjoji Wuta A Iyakar Kwara Da Kogi
Mataimakin kwamandan Hisba a bangaren ayyuka na musamman Dr Mujahedeen Aminuddeñ Abubakar shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga Jaridar Inda Ranka
Sanarwar ta kara da cewa Jami’an Hisbah sun isa wurin ne inda suka tarwatsa taron tare da kama mutane 25 — maza 18 da mata 7 — waɗanda ake zargi da hannu a lamarin.
Wasu daga cikin mutanen da aka kama, a cewar majiyar, sun fito daga unguwanni daban-daban na cikin Kano, ciki har da Sheka, Yar Gaya, da Kofar Nasarawa.
Hukumar ta ce ta garzaya da su ofishin Hisbah domin gudanar da bincike.
-
News1 day ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News17 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
