Connect with us

News

’Yan Yahoo’ Matasa Ne Masu Basira Da Suke Bukatar Shiryarwa Ba La’anta Ba —Peter Obi

Published

on

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya bayyana cewa matasan da ake kira ‘yan Yahoo ba marasa tarbiyya ba ne gaba ɗaya, domin wasu daga cikinsu matasa ne masu basira da ƙwazo, waɗanda za su iya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban ƙasa idan aka shiryar da su ta hanya mai kyau.

Obi ya yi wannan bayani ne yayin wani taro da aka kira “Golden Health” da aka gudanar a Onitsha, Jihar Anambra, inda ya ce basira da jarumtakar da wasu daga cikin matasan ke da ita na iya zama ginshiƙin kirkire-kirkire da ci gaban tattalin arzikin ƙasa, idan aka tsara su yadda ya kamata.

Advertisement

Majalisar Dokoki Ta Amince Da Shirin Kirkirar Sabbin Jihohi Shida A Najeriya

Ya ce, “Na dawo daga Birtaniya domin halartar wannan taro, wanda ke da nufin inganta halayyar matasa da jagoranci na gaskiya. Amma gaskiya ne, Najeriya ba za ta ci gaba ba muddin muna ɗaukaka rashawa da rashin gaskiya.”

Tsohon gwamnan Anambra ɗin ya jaddada cewa dukiya ba ta taƙaitu ga tara kuɗi kawai ba, domin a cewarsa, “ainihin dukiya ita ce wadda ke gina mutum da al’umma ta hanyar ilimi, rage talauci da samar da damammaki ga wasu.”

Advertisement

Ya kuma shawarci matasa da su guji son hanya ta gaggawa wajen neman arziki, su rungumi aiki tukuru da gaskiya, yana mai cewa “kasashe ba sa ginuwa da mu’ujiza, sai da mutane masu aiki da hangen nesa.”

A ƙarshe, Obi ya bukaci gwamnati da shugabanni su tabbatar da adalci da daidaito ga kowa, tare da cewa ci gaban ƙasa yana buƙatar haɗin kai ba tare da nuna bambancin kabila ko addini ba.

Advertisement

 

 

Advertisement

DAILY POST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending